Header Ads Widget

 


Gidauniyar Garkuwan Sha’iran Birni da Kewaye,Ta Horas da Mata Sama da 750 Sana’o’in Hannu, Ta Nemi Tallafin Gwamnati

By Hassan Ibrahiim 


Shugabar Gidauniyar Garkuwan Sha'iran Birni da Kewaye, Sayyada Jamila, ta bayyana muhimmancin gidauniyoyi wajen tallafawa al’umma, musamman mata marasa ƙarfi, marasa lafiya, marayu da tsofaffi, domin taimaka musu wajen samun sauƙi da dogaro da kai a rayuwa.

Ta ce gidauniyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen inganta zamantakewar al’umma, musamman ta hanyar koyar da mata ƙananan sana’o’in hannu da za su taimaka musu wajen samun abin dogaro da kansu.

A cewarta, ya kamata gwamnati ta kula da irin waɗannan gidauniyoyi tare da tallafa musu, kasancewar a wasu lokuta suna taimakawa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati.

Sayyada Jamila, wadda ita ce shugabar gidauniyar kuma shaira mai yabon Annabi Muhammad (SAW), ta ce an haife ta a garin Zariya, inda ta yi karatun firamare da sakandare, sannan taje karatun Nursing.

Ta ce yanayin da wasu mata, marayu da tsofaffi suka tsinci kansu a ciki ne ya sa ta fara tunanin kafa gidauniya da za ta tallafa wa mata ta hanyar koyar da su sana’o’in hannu, domin su samu abin dogaro da kansu a rayuwa.

A cewarta, gidauniyar ta gudanar da ayyuka daban-daban tare da kai ziyara wurare da dama ciki da wajen Jihar Kaduna domin samun shawarwari kan yadda za a gudanar da ayyukan gidauniyar yadda ya kamata, abin da ta ce ya taimaka wajen samun nasara.

Sayyada Jamila ta bayyana cewa idan mace tana da sana’a, hakan na taimaka mata wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin gidanta, saboda tana iya samun abin da za ta dogara da shi.

Ta ce a farkon kafa gidauniyar, ba ta samu wani tallafi daga wajen kowa ba, inda ta fara da ɗan albashin da take samu da kuma kuɗin kasuwancinta, kafin daga baya ta samu gudunmawa daga bangaren ADC, kasancewar gidauniyar tana gudanar da ayyukanta ne ba tare da neman kuɗi daga masu cin gajiyar horon ba.

Ta ce a farko an fara da mutane 100 da aka koyar da sana’o’in hannu daban-daban, daga baya adadin ya ƙaru zuwa 700, har zuwa lokacin da aka kammala horar da mutane 750.

Ta bayyana cewa tun daga wannan lokaci ba ta samu wani gagarumin tallafi ba, sai dai daga Sakataren Ƙaramar Hukumar Zariya, Hon. Shuaibu Abdullahi Mai-Kanta, wanda ta ce ya taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa gidauniyar, kuma yake shirye a duk lokacin da ake shirin yaye mutanen da aka koyar da sana’o’in hannu.

Ta kuma bayyana cewa ɗan majalisar da ke wakiltar cikin Birnin Zariya, Hon. Mahmud Lawal Isma’ila Bola-Ige, ya tallafa wa gidauniyar, tare da Malam Muhammad Lawal Mai Elser, inda aka samar da tallafin karatu ga mutane 20 domin su ci gaba da karatunsu.

Shugabar gidauniyar ta yi kira ga gwamnati, masu ruwa da tsaki, sarakuna da masu hannu da shuni da su tallafa wa gidauniyar, domin ta ci gaba da taimaka wa marayu da mata ta hanyar ba su horon sana’o’in hannu.

Ta ce burin gidauniyar shi ne horas da kusan mutane 1,000, amma nauyin da ke kanta ya yi yawa, musamman ganin cewa a halin yanzu mutane 259 ne suka yi rajista, yayin da sama da mutane 300 ke da sha’awar shiga gidauniyar amma ba su da kuɗin yin rajista.

Ta ƙara da cewa ita ce ke samar da kayayyakin da ake amfani da su wajen koyar da waɗannan sana’o’in hannu, abin da ya sa ake buƙatar ƙarin tallafi daga gwamnati da sauran masu hannu da shuni.


Post a Comment

0 Comments