Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun samu nasarar kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar.
Gidan talbijin na Channels ya ruwaito ’yan sandan su na cewa sun kama ɗan bindigar mai suna Mati Bagio ne bayan kimanin shekara 11 suna nemansa ruwa a jallo.
Kakakin rundunar, Mansir Hassan ya ce Bagio mai kimanin shekara 34 ya daɗe yana addabar yankunan Giwa da Hunkuyi a Kaduna, da Faskari da Dandume da Funtua a jihar Katsina.
"Mun kama shi ne a ranar 18 ga watn Yulin tare da makamai da dama irin su alburusai da bindiga ƙirar AK-47 da sauran su."


0 Comments