APC ta yi Nasara na zaɓen cike gurbi na Zariya da Basawa
Daga Hassan Ibrahim
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na mazaɓar Zaria Kewaye da Basawa da aka gudanar ranar Asabar 16 ga Augusta, 2025.
Daily Naija Updates ta ruwaito cewa, yayin bayyana sakamakon zaɓen mazabar Zariya Kewaye, babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Balarabe Abdullahi na jami'ar Ahmadu Bello (ABU), ya bayyana Isa Haruna Babanyaya na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’u 26,613.
A matsayi na biyu, ɗan takarar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Nuhu Sada Abdullahi, ya samu ƙuri’u 5,721, yayin da ɗan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Mamuda Abdullahi Wappa, ya samu ƙuri’u 5,331.
Haka zalika, yayin bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen cike gurbi na mazabar Basawa, Farfesa Nasiru Rabiu ya bayyana ɗan takarar jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara.
Ya na mai cewa, jam'iyyar APC ta samu ƙuri’u 10,926, yayin da babbar jam’iyyar hamayya wato PDP ta samu ƙuri’u 5,499.

0 Comments