Daga Hassan Ibrahim
A ranar Asabar 22 ga watan Nuwamba, shekara ta 2025, Jaridar Gombe Ayau ta karrama Alhaji Ahmed Suleiman (Chairman/CEO ) Babal Furniture's da lambar yabo na girmamawa,bisa irin gudunmuwar da yake bayarwa na cigaban al'umma da kuma taimakawa matasa na sana'a dan samun abinda zasu dogara da shi a rayuwa.
Jim kadan bayan amsar lambar yabon Alhaji Ahmed Suleiman ya yi godiya ga Allah SAW na ganin wannan rana, da kuma yin godiya ga wannan kamfanin jarida.
Ya yi kira ga matasa wajen Jajircewa akan sana'o'i kasancewar ita ce hanya mai Éorewa a rayuwar su.
Ya jaddada muhimmancin dake akwai wajen kira ga masu hannu da shuni domin bayar da gudunmuwar su na samar da al'umma ta gari acikin zamantakewa na rayuwa.
Taron ya samu halartar ʓan uwa da abokan arziki.
Ga kaÉan daga cikin hotunan da aka Éauka lokacin bayar da lambar yabon

0 Comments