Daga Hassan Ibrahim
Madrasatul Madinatul Ahbab Nursery and Primary School da ke Kakuri, Jihar Kaduna, ta gudanar da taron Walimar Saukar Alƙur’ani Mai Girma karo na 30 a ranar Lahadi, 14 ga watan Disamba, 2025.
Taron ya gudana ne a harabar makarantar da ke kan titin Dawakin Bassa, Kakuri.
A yayin tattaunawarsa da Daily Naija Updates, Shugaban Makarantun Madrasatul Madinatul Ahbab na ƙasa da na ƙetare, Khalifah Shaikh Ɗayyid Shaikh Haruna Rasheed, ya yi kira ga masu hannu da shuni a cikin al’umma da su sadaukar da dukiyoyinsu domin tallafa wa ci gaban makarantun Islamiyya.
Ya jaddada muhimmancin tallafa wa irin waɗannan makarantu, yana mai bayyana cewa hakan na da babban lada a duniya da kuma gobe kiyama.
A cewarsa, wannan hanya ce mai muhimmanci ta bunƙasa addinin Musulunci da kuma gina ingantacciyar al’umma ta Musulmi.
Khalifah Shaikh Haruna Rasheed ya kuma yi kira ga shugabanni masu riƙe da madafun iko da su ba da kulawa ta musamman ga makarantun Islamiyya,
yana mai cewa ɗaliban da suka samu tarbiyya a irin waɗannan makarantu ana sansu da kyakkyawar ɗabi’a, wadda ke taimakawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin al’umma da gwamnati, tare da haifar da ‘yan ƙasa nagari da ake alfahari da su.
Haka zalika, ya shawarci iyaye da su ci gaba da kula da tarbiyyar ‘ya’yansu tare da ba su ingantaccen ilimi.
Ya ce babbar ni’ima ce ga iyaye su ga ‘ya’yansu na daga cikin waɗanda Allah Ya azurta da ilimin Alƙur’ani Mai Girma, yana mai ƙara da cewa ilimin addini shi ne mafi girman abin da uba zai bai wa ‘ya’yansa, musamman a wannan lokaci da ake ciki.
A nasa jawabin, Alhaji Shehu Tijjani, Chiroman Zazzau kuma Hakimin Gundumar Makera, wanda Magajin Garin Kakuri, Alhaji Nura Muhammad Sadau, ya wakilta, ya yi kira ga matasa da su tashi tsaye wajen neman ilimin addini domin sanin yadda za su bauta wa Allah (SWT) yadda ya kamata.
Shi ma Injiniya Shehu Abubakar, ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar, ya bayyana godiyarsa ga Allah (SWT) bisa ci gaban da makarantar ke samu, musamman ta fuskar ƙaruwa a yawan ɗalibai da malamai.
Ya ce iyaye sun fahimci muhimmancin tura ‘ya’yansu makaranta, la’akari da ingancin tsarin koyarwa da ya dace da zamani.
Ya kuma jaddada buƙatar tsofaffin ɗalibai su zama jakadu nagari na makarantar tare da haɗa kai wajen bunƙasarta.
A ɓangaren nasa, Shugaban makarantar, Malam Salisu Ibrahim Daura, ya bayyana cewa tun kafuwar makarantar sama da shekaru arba’in da suka gabata, ta samu nasarori da dama wajen tarbiyya da koyar da yara.
Sai dai ya bayyana cewa makarantar na fuskantar ƙalubale, musamman rashin cika alƙawarin biyan kuɗin makaranta daga wasu iyaye, lamarin da ke kawo cikas ga walwalar malamai.
A yayin taron, an yaye ɗalibai 30 da suka sauke karatun Alƙur’ani Mai Girma. Wasu daga cikin ɗaliban da aka yaye, ciki har da Zannura Muhammad da Amina Lawal, sun bayyana farin cikinsu da godiya ga Allah bisa wannan babbar nasara.
Taron ya samu halartar malamai, ɗalibai, iyaye da kuma manyan baƙi daga sassa daban-daban na al’umma.

0 Comments