Header Ads Widget

 


Manajan Daraktan S. Usman Estate Ya Yi Kira Ga Matasa Su Rungumi Sana’o’i da Kasuwanci Domin Dogaro da Kai


Daga Hassan Ibrahim 

Manajan Daraktan kamfanin S. Usman Estate Construction & Co. Ltd, Alhaji Sale Usman, ya shawarci matasa da su rungumi koyon sana’o’i da kasuwanci, komai ƙanƙantarsu, domin su dogara da kansu tare da kula da iyalansu.

Sale Usman, wanda ofishinsa ke unguwar Zangon Shanu a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa.

Alhaji Sale Usman ya ce yana da matuƙar muhimmanci ga matasa a wannan zamani da ake ciki su tashi tsaye da jajircewa wajen koyon sana’o’in hannu, domin su samu hanyar dogaro da kai a rayuwa, har ma su taimaka wa wasu.

Ya jaddada muhimmancin matasa su zama mutane nagari da za a yi alfahari da su a cikin al’umma. A cewarsa, babban abin da ya kamata su riƙe a rayuwarsu shi ne sanya tsoron Allah a zukatansu.

Ya kuma bayyana cewa yana da muhimmanci gwamnati a matakai daban-daban ta samar da tsare-tsare da shirye-shiryen da za su tallafa wa matasa ta fannoni daban-daban na rayuwa.

Alhaji Sale Usman ya nuna godiyarsa ga Allah bisa damar da Ya ba shi duk da kasancewarsa matashi, yana mai cewa hakan ya taimaka masa wajen samun halal da kuma amincewa da yarda daga shugabannin al’umma.

Ya tabbatar da cewa kafin fara harkokinsu na kasuwanci, sun tabbatar sun mallaki dukkan sahihan takardu da amincewar doka da ake buƙata, domin kauce wa matsaloli tare da tabbatar da gaskiya da amana a mu’amalolinsu.

Ya ƙara da cewa harkar hayar gidaje da sayar da filaye sana’a ce ta halal, mai gaskiya kuma abin dogaro, wadda ake gudanarwa bisa ƙa’idoji da dokoki da aka tanada, duk da cewa a wasu lokuta tana fuskantar ƙalubale.

Saboda haka, ya yi kira ga hukumomin ƙananan hukumomi da su ba su haɗin kai domin gudanar da kasuwancinsu cikin tsari da lumana.

Haka zalika, wasu sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma sun bayyana kwarin gwiwarsu kan gudunmawar da Alhaji Sale Usman ke bayarwa a yankin, tare da shaida kyawawan halayensa, gaskiyarsa da mutuntakarsa ga jama’a.

Shugaban Elders Community Security Forum na Zango, Muhammad Ahmed Muhammad, ya yaba da kyawawan ɗabi’un matashin ɗan kasuwar, musamman ƙoƙarinsa na rage yawaitar shaye-shaye a yankin.



Post a Comment

0 Comments