Header Ads Widget

 


Matasa Su Yi Soyayyar Annabi Da Gaske, Ba Ta Baki Kaɗai Ba — Kabir Hafiz


Daga Hassan Ibrahim 


Sayyadi Kabir Hafiz Dan Bature, ya bayyana cewa maganar ƙaunar Manzon Allah (SAW) abu ce da aka gada daga gida, domin tun daga limamai zuwa iyaye da kakanni, duk a irin wannan turba aka taso.

Ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a garin Zariya.

Sayyadi Kabir Hafiz ya bayyana cewa  ƙaunar Annabi (SAW) wata daraja ce da aka gada  kuma buri ne da aka taso ana ɗauke da shi tun ƙuruciya. 

Don haka, ya shawarci matasa da su riƙi soyayyar Manzon Allah da gaskiya a zukatansu, su nuna ƙauna ta gaskiya ba ta baki kaɗai ba, domin babu inda ba za su kai ba idan suka yi riko da koyarwarsa
.
Dangane da sanya sunan da Gwamnan Jihar Kaduna ya yi na marigayi Shaikh Dahiru Usman Bauchi, Kabir ya ce abin farin ciki ne matuƙa, inda ya yabawa gwamnan bisa yin abin da ya dace, na sauya sunan Kwalejin Nazarin Larabci ta Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) zuwa sunan marigayi Shaikh Dahiru Usman Bauchi, domin tuna irin gudummawarsa ga ilimi da addini.

Ya ƙara da cewa, duk wani abin da aka yi na girmama marigayi Shaikh Dahiru Usman Bauchi abu ne da ya dace, kuma al’umma na godiya ƙwarai da gaske.

Ya jaddada cewa bikin Mauludi ibada ce ta nuna soyayya ga Manzon Allah (SAW), ba wurin tayar da fitina ko rikici ba.

Ya ce duk abin da ake yi saboda ƙaunar Annabi (SAW), alheri ne da albarka, kuma duk wanda aka bi saboda soyayyarsa ga Manzon Allah, babu arziki ko rahamar da ba zai samu ba. Allah (SWT) kan azurta shi da falala ta duniya da ta lahira.

A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar Musulmi gaba ɗaya da su ci gaba da gudanar da Mauludi a matsayin ibada da haɗin kai, tare da kauce wa duk wani abu da zai ɓata manufar bikin.



Post a Comment

0 Comments