Ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar birnin Zariya kuma shugaban kwamitin ilimi na majalisar dokokin jihar Kaduna Honorabul Mahmud Lawal Sama’ila (Bola Ige) ya miƙa saƙon ban gajiya ga Gwamna Uba Sani bisa ziyarar da ya kawo a Zariya na kaddamar da tituna biyu wanda ɗan majalisar ya kawo a ƙaramar hukumar Zariya
“Titin da ya taso daga Amaru zuwa Magajiya zuwa unguwar Liman da Albarkawa a cikin birnin na Zariya, da kuma titin da ya taso daga Audi zuwa garin Kaku, ina fatan mai girma Gwamna ya koma gida lafiya tare da fatan Allah ya ƙara zumunci”
Ɗan Majalisa wanda kuma shi ne mataimakin shugaban mai tsawatarwa na majalisar ya kuma ƙara nuna farin cikinsa bisa amincewar da Gwamnan ya yi na rokon da ya yi mishi na aikin ƙarin tituna uku da ya yi, titin da ya taso daga babban dodo zuwa Durumi zuwa unguwar juma zuwa kuma kofar kuyanbana, da Rimin tsiwa ya wuce ƙaura da ƙofar gayan a cikin birnin Zariya.
“Titin da mai girma Gwamna ya yi alkawarin zai yi shi ne wanda ya taso daga ƙofar Gayan ya wuce har garin Igabi inda ya ratsa cikin garuruwa 59 da kuma kananan hukumomi guda Uku”

0 Comments