Header Ads Widget

 


Jaridar Taskira Ta Karrama Makumbo Memorial Clinic and Maternity, Zaria Saboda Gudunmuwar Lafiya ga Al’umma


Daga Hassan Ibrahim 


Jaridar Taskira ta karrama Makumbo Memorial Clinic and Maternity, Zaria bisa gudunmuwar da asibitin ke bayarwa wajen tallafa wa al’umma ta fannin kiwon lafiya, a wani biki da aka gudanar ranar Asabar, 4 ga Afrilu, 2026 a cibiyar matasa da ke Tudun Wada, Zaria.

Da yake jawabi jim kaÉ—an bayan karÉ“ar lambar yabon, Sakataren asibitin, Falalu Balarabe, ya bayyana matuÆ™ar farin cikinsa bisa yadda aka zaÉ“i asibitin nasu duk da yawan cibiyoyin lafiya da ke akwai, yana mai cewa hakan ya nuna an lura da irin hidimar jin Æ™ai da suke yi wa jama’a.

Falalu ya danganta wannan nasara da jagoranci nagari na shugaban asibitin, Dakta Ado Zakari Muhammad, wanda a cewarsa koyaushe yana jaddada musu cewa al’umma su ne a gaba fiye da komai, kuma duk wata dama da za su samu su taimaka wa marasa Æ™arfi to su yi hakan ba tare da wata shakka ba.

Ya Æ™ara da cewa duk da kasancewar asibitin mai zaman kansa ne, suna karÉ“ar marasa lafiya ko da ba su da kuÉ—i, inda ake ba su kulawa ta gaggawa, sannan a tattauna batun kuÉ—i daga baya idan hali ya ba su dama. 

Wannan tsarin, a cewarsa, ya taimaka wajen ceto rayuka da dama da kuma sauÆ™aÆ™a wa jama’a wahalhalun neman lafiya.

Sakataren ya yi kira ga sauran asibitoci masu zaman kansu da su É—auki irin wannan tsari na tausayi, su fifita rayuwar al’umma a kan ribar kuÉ—i, domin hakan ne zai kawo sauyi mai ma’ana a harkar kiwon lafiya tare da Æ™ara kusantar jama’a da cibiyoyin lafiya.

Ya kuma bayyana cewa wannan karramawa za ta Æ™ara musu Æ™aimi da jajircewa wajen ci gaba da hidimtawa al’umma, ganin cewa ayyukan da suke yi sun kai matakin da har kafar yaÉ—a labarai ta ga dacewar girmama su.
An gudanar da taron karramawar ne cikin yanayi na farin ciki da halartar jama’a da dama daga sassa daban-daban na Zaria da kewaye, inda aka yaba da rawar da asibitin ke takawa wajen cike gibin da ake fuskanta a É“angaren kiwon lafiya.

Post a Comment

0 Comments