Header Ads Widget

 


Jaridar Taskira Ta Karrama ASP Mustapha Ibrahim Datti a Zariya



Daga Hassan Ibrahim 


Jaridar Taskira ta karrama Mataimakin Sufiritandan na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya, Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), ASP Mustapha Ibrahim Datti, wanda ke rike da mukamin O/C Outpost Jushi a Zariya, bisa jajircewarsa da gudummawar da yake bayarwa wajen tabbatar da tsaro a yankin.

An gudanar da taron karramawar ne a ranar Asabar, 9 ga watan Mayu, 2026, a cibiyar matasa da ke Tudun Wada, Zariya, inda ‘yan uwa da abokan arziki suka halarta domin shaida wannan gagarumar karramawa.

Da yake jawabi bayan karbar lambar yabon, ASP Mustapha Ibrahim Datti ya bayyana farin cikinsa bisa wannan karramawa, yana mai cewa duk wanda Allah Ya karrama, ya kamata ya nuna godiya da farin ciki.

Ya ce wannan karramawa abin alfahari ne a gare shi da iyalansa baki daya, musamman ganin cewa wannan ita ce karramawa ta biyar da ya samu daga wurare daban-daban.
ASP Datti ya kara da cewa, kwarewarsa a fannin horaswa (training) ta samo asali ne sakamakon aikin da ya yi a sassa daban-daban na kasar nan, ba a Arewa kadai ba har ma da Kudancin Najeriya.

Ya yi kira ga abokan aikinsa da su rike gaskiya da amana a duk inda suke, yana mai cewa duk wanda ya rike gaskiya, Allah Zai taimake shi a dukkan lamuransa.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba su ikon tafiya a kan turbar gaskiya da adalci, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalolin rashin tsaro a wasu sassan kasa.

ASP Datti ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa da yardar Allah, yankin Jushi a Zariya zai ci gaba da kasancewa wuri na zaman lafiya a lokacin da yake rike da wannan mukami.
Haka kuma, ya yi kira ga al’umma da su rika bai wa jami’an tsaro bayanan sirri kan duk wani shiri na aikata barna kafin ya faru, yana mai tabbatar da cewa a shirye suke koyaushe wajen ba da gudunmawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.



Post a Comment

0 Comments