Bayan shafe shekaru arba'in da barin azuzuwan Makarantar Government Day Secondary School (GDSS) Zariya, tsofaffin ɗaliban shahararren ajin 1986 sun sake haɗuwa cikin gagarumin biki domin murnar cika shekaru 40 da kammala karatunsu, tare da mayar da taron wani dandali na kira ga sabunta zuba jari a fannin ilimi da bunƙasa shugabanci a Arewacin Najeriya.
Taron wanda ya gudana a Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, ya haɗa fitattun tsofaffin ɗalibai, sarakunan gargajiya, masana ilimi, jami'an soja, manyan jami'an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, inda suka yi waiwaye kan muhimmiyar rawar da ilimi ke takawa wajen gina al'umma.
Da yake gabatar da muƙalar jigo mai taken "Ilimi a Matsayin Ginshiƙin Shugabanci", Shugaban Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, Farfesa Adamu Ahmed wanda Daraktan Cibiyar Ilimi ta jami'ar, Farfesa Abubakar Jumare ya wakilta, ya jaddada cewa taron bai kamata ya tsaya kan murna kawai ba, sai dai ya zama wata dama ta tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen farfaɗo da ilimi, musamman a Arewacin Najeriya inda yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma ƙarancin ƙwarewar ilimi suka zama babban ƙalubale.
Ya buƙaci membobin ajin da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai, su riƙa taimakon juna tare da mayar da wani ɓangare na gudummawarsu ga tsohuwar makarantar tasu ta hanyar tallafin karatu, shirye-shiryen jagoranci da kuma sauran ayyukan ilimi da za su zaburar da al'ummomi masu tasowa.
A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, wanda Garkuwan Ayyukan Zazzau, Injiniya Balarabe Ibrahim Musa ya wakilta, ya bayyana cewa ilimi shi ne tubalin ci gaban al'umma.
Ya yaba da ƙoƙarin gwamnati da masarautun gargajiya wajen faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi, tare da yin kira da a ci gaba da addu'o'i domin samun zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ƙasa.
Ya ƙara da cewa ba za a samu ci gaba mai ɗorewa ba sai an ci gaba da saka hannun jari a fannin ilimi, yana mai bayyana cewa Masarautar Zazzau na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar ilimi domin kyakkyawar makoma.
Da yake jawabi Mataimakin Shugaban Jami'ar ilimi ta Tarayya da ke Zariya, Farfesa Suleiman Balarabe, ya nuna damuwa kan yadda inganci da tarbiyya suka ragu a makarantu da dama na gwamnati, musamman makarantun kwana.
Ya danganta wannan matsala da cin hanci da rashawa da kuma rashin kyakkyawan tsari na gudanarwa, yana mai cewa makarantu irin su GDSS Zariya a baya sun kasance cibiyoyin da suka samar da mutane masu tarbiyya, nagarta da manyan nasarori waɗanda daga baya suka zama shugabanni a fannoni daban-daban na rayuwa.
Ya jaddada cewa gina shugabanci tsari ne mai ɗaukar lokaci wanda ke buƙatar jagoranci da tarbiyya daga tsara zuwa tsara, yana mai bayyana hakan a matsayin wata muhimmiyar hanya ta ci gaban al'umma.
Shugaban makarantar GDSS Zariya, Malam Zubairu Aminu, ya yi bayani kan tarihin ci gaban makarantar tare da bayyana nasarori da dama da aka samu tsakanin shekarun 2022 zuwa 2025.
Sai dai ya bayyana wasu manyan ƙalubalen da makarantar ke fuskanta, ciki har da rashin ingantaccen tsarin magudanar ruwa da kuma ƙarancin kwamfutoci da kayan aikinsu, inda ya yi kira ga tsofaffin ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki da su tallafa wajen inganta ababen more rayuwa da samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, Shugaban Kwamitin Shirya Taron kuma Sarkin Noman Zazzau, Aliyu Bamalli, ya bayyana taron a matsayin bikin cika shekaru arba'in na gwagwarmaya, nasarori, ƙalubale da kuma abubuwan tunawa da suka haɗa membobin ajin.
Ya bayyana cewa daga cikin ɗalibai 345 na asalin ajin shekarar 1986, mutum 36 sun rasu, inda ya yi musu addu'ar samun rahama tare da ƙarfafa gwiwar waɗanda suke raye da su haɗa kai domin gina kyakkyawar makoma.
Haka kuma ya sanar da kafa ƙungiyar zumunci ta membobin ajin tare da ƙaddamar da duk mahalarta taron cikin shahararriyar "Class of 1986 Hall of Fame", yana mai nuna fatan cewa taron zai ƙara ƙarfafa zumunci da kuma zaburar da membobin wajen ba da gudummawa ga al'umma.
A jawaban su daban-daban, Rear Admiral Muhammad Miftah Abdullahi mai ritaya, Rt. Hon. Ahmed Mohammed na Hukumar Kula da Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya ta Babban Birnin Tarayya da kuma Farfesa Ahmed Mohammed Bakori na Jihar Katsina sun bayyana farin cikinsu na sake haɗuwa da abokan karatunsu bayan shekaru arba'in, tare da alƙawarin ci gaba da tallafa wa tsohuwar makarantar tasu domin samar da yanayi mai kyau ga koyarwa da koyo.
An kammala taron ne da sabon ƙuduri daga membobin Rugby Class of 1986 na ci gaba da kare martaba da gadon makarantar tasu tare da bayar da gudummawa mai ma'ana ga makomar ilimi a Najeriya.

0 Comments