Header Ads Widget

 


Nasara Daga Allah Ne, Kuma Naji Daɗi Da Ya Bani Wannan Nasara - Abdullahi Mamuda Wappah

 


Daga Hassan Ibrahim

Zaɓaɓɓen ɗan takarar jam'iyyar PDP na mazaɓar Zaria Kewaye a zaɓen fidda gwani da ya gabata, Alhaji Abdullahi Mamuda Wappah ya miƙa godiya ga Allah SWT da ya nuna masa wannan rana da kuma ya bashi nasara a zaɓen da ya gabata.

Ya yi godiya ta musamman ga shuwagabannin jam'iyya na PDP tun daga matakin jiha, Ƙananan hukumomi zuwa  Mazaɓu ,da Deliget da suka gudanar da zaɓen.

“Kasancewar Nasara daga Allah ne kuma naji daɗi da ya ba ni wannan Nasara,babban fata na shine  Allah ya bani Nasara a zabe mai zuwa”, Inji shi.

Abdullahi ya kuma godewa al'umma waɗanda suka yi masa fatan alkhairi da adduo'i dan samun nasara, babu abinda zance sai dai in ce Allah ya saka musu da alkhairi.

Ya kuma ƙara da cewa, su kuma abokanan takara na, ina yi musu fatan alkhairi kuma ina neman shawarwari daga gare su domin tunkarar zaɓe na gaba.

Ina kira ga al'umma da su fito ranar 16 ga watan Augusta, shekara ta 2025, dan ganin sun mara mana baya domin kaiwa ga gaci.

“Yanda nike matashi ina so matasa su bani goyon baya mu ci wannan zabe, su gujewa duk wani abu da ka iya tayar da zaune tsaye lokacin zaben”, a cewar sa.

Ya kuma yi addu'ar samun dawwamammen zaman lafiya ƙaruwar arziki da ci gaba mai ɗorewa a masarautar Zazzau, jihar Kaduna da ma Nijeriya baki daya.

Usman Jibril wanda aka fi sani da Rubuci, babban Darakta na tafiyar ɗan takarar yace abin godiya ne ga Allah SWT yanda aka gudanar da zaɓen cikin lafiya da kwanciyar hankali.

Kazalika ya mika godiya da jinjina ga Delegates, masu ruwa da tsaki, shuwagabannin jam'iyya na PDP tun daga matakin jiha zuwa ƙananan Hukumomi da Mazaɓu, yanda suka bada goyon baya dan ganin wannan zaɓe ya tabbata cikin lafiya da kwanciyar hankali.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga sauran abokan takara da su zo a haɗa hannu a matsayin ƴan ƙaramar hukumar Zaria dan fitar da kitse a wuta na baiwa jam'iyyar PDP goyon baya kasancewar za'a samu canji na gari.

Post a Comment

0 Comments