A ranar Juma’ar ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa jihar Kano domin jajantawa iyalan marigayi dattijon ƙasa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Aminu Ɗantata.
Jirgin shugaban kasa Tinubu ya sauka a filin jirgin saman Aminu Kano da misalin ƙarfe 3:30 na rana, inda gwamnan Kano, Abba Yusuf, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi.
Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, na cikin jami’an gwamnati da suka raka shugaban ƙasar a wannan tafiya.
A yayin ziyarar tasa, ana sa ran Tinubu zai kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata tare da jajanta wa jama’a da gwamnatin jihar Kano bisa rasuwar ɗan kasuwan.
Dantata, hamshakin mai masana'antu kuma mai taimakon jama'a, ya rasu ne a ranar 28 ga Yuni, 2025, a Abu Dhabi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
A lokacin, Tinubu ba ya ƙasar, amma ya umurci tawaga karkashin jagorancin ministan tsaro, Mohammed Badaru, da su halarci jana’izar da za a yi a ƙasar Saudiyya domin nuna girmamawa.


0 Comments