Bamu Da Ƙalubale Da Yardan Allah.Hon. Tukur Salisu Kakeyi
Daga Hassan Ibrahim
Tsohon ɗan takaran kujeran majalisar dokoki na jihar Kaduna mai wakiltar Zaria Kewaye, Hon. Tukur Salisu Kakeyi ya ce jam'iyyar su ta PDP ba su da wani ƙalubale a zaɓen cike gurbi da ke tafe sati mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da Daily Naija Updates, Jim ƙadan bayan kammala taron bayar da tuta na ɗan takaran kujeran majalisar dokoki na jihar Kaduna na Jam'iyyar PDP, na mazaɓar Zariya Kewaye, wanda ya gudana a Cibiyar Matasa wato Youth Center, da ke Tudun Wada, Zaria.
Hon. Salisu Tukur Kakeyi, bayan Godiya ga Allah (SAW) da yayi na ganin wannan rana mai muhimmanci ga ɗaukacin ƴaƴan jam'iyyar PDP na mazaɓar Zaria Kewaye, Yace bamu da wani ƙalubale a gaban mu,na zaɓen da ke tafe, kasancewar mun dogara ga Allah ne, domin shi ke bayar da mulki ga wanda ya so.adan haka Nasara ta mu ce da Yardan Allah.
Ya kuma ƙara da cewa, wannan halin da ake ciki in Allah ya so ya yarda, al'umma sun san abinda ya faru a baya, sun san abinda ke faruwa yanzu, sun san abinda zai faru gobe, wanda Allah ne ya sani amma daga yanzu, ka ke gane cewa tafiyar gobe me zai faru.
"Misali zan yi maka, yau kana siyan buhun taki dubu ɗari DAF, amma ga sabon masara ta fito akan dubu goma sha takwas, wannan kadai ya ishe ka amsa.In ji shi."
Daga ƙarshe, ɗan siyasan, ya shawarci ƴaƴan jam'iyya PDP da al'ummar Zaria kewaye su kada wa jam'iyyar PDP wato Abdullahi Mamuda Wappah kasancewar shine mafita ga al'umma.
"Baballe alheri ne, akwai Nasara da yardar Acewar sa."

0 Comments