Matasa su nemi ilimin addini da na Zamani domin samun rayuwa ingantacce. Malam Yusha'u Aliyu.
Daga Hassan Ibrahim
Malam Yusha'u Aliyu da ke Anguwar Nagoyi, cikin ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduna, ya shawarci matasa dasu tashi tsaye na neman ilimin addini da na zamani.
Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan amsar lambar yabo daga jaridar Gombe AYau.
Malamin ya na mai cewa ilimi shine jigo na rayuwa kasancewar shine fitilar dake haskaka wa a rayuwar ɗan Adam.
"Kasancewar idan suka dage da neman ilimi zasu fita daga cikin dukkan wani kangi na rayuwa'.In ji shi.
Ya bayyana cewa Idan ilimi ya samu babu sauran talauci.a rayuwar ɗan Adam.
Dangane da lambar yabo da aka basa,malamin ya yi godiya ta musamman ga wannan jarida.
Acewarsa yanda mutane ke yi mana zato na alkhairi, to babu abinda zamu cewa Allah sai godiya.

0 Comments