Header Ads Widget

 


Gidauniyar Uwar - Al’umma Ta Karrama Sakataren Karamar Hukumar Zariya Bisa Ƙoƙarinsa na Cigaban Al’umma


Daga Hassan Ibrahim 

An gudanar da taron walima da bayar da lambobin yabo domin karrama masu riƙe da muƙaman siyasa, inda aka bai wa Sakataren Ƙaramar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi Mai Kanta, lambar yabo ta musamman. 

An gudanar da taron ne a Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Zaria.

Da take jawabi a wajen taron, Hajiya Asma’u Minka'ila Salisu, Shugabar  Gidauniyar Uwar Al’umma Charity and Awareness Forum, ta ce an shirya taron ne domin nuna farin ciki da godiya ga Sakataren bisa ƙoƙarinsa na samar da damammaki ga matasa.

Ta ce irin waɗannan ayyuka sun rage nauyi ga gwamnati tare da zama abin tunawa a tarihin cigaban al’umma.

Ta bayyana cewa Gidauniyar na aiki ne a fannoni guda huɗu da suka haɗa da yaƙi da jahilci, wayar da kan iyaye mata da mata gaba ɗaya, kula da mata da ƙananan yara, da kuma taimakon marayu. 

Ta ƙara da cewa Gidauniyar ta taimaka wa Marayu da suka daina zuwa makaranta sakamakon rashin gata, inda ta ɗauki nauyin komawarsu makaranta, ta dinka musu kayan makaranta (uniform) da samar da sauran buƙatu.

Hajiya Asma’u ta ce Gidauniyar na tsayawa da ƙafafunta ne ta hanyar haɗin kai da tallafin mambobinta. 

Ta yi kira ga masu hali da su bayar da gudunmawa domin ɗorewar wannan aikin alheri.

Shi ma Muhammad Musa Arɗo, Mataimakin Shugaban Gidauniyar, ya ce an shirya taron ne domin gode wa Allah da kuma nuna godiya ga waɗanda ke amfana da ayyukan gidauniyar. 

Ya ce an kuma bayar da lambar yabo ga “uban wannan tafiya,” wato Sakataren Ƙaramar Hukumar Zaria.

Ya bayyana cewa, suna da tsare-tsare da dama na shekarar 2025, ciki har da shirin mayar da yara marasa galihu makaranta. 

Sauran shirye-shiryen sun haɗa da koyar da sana’o’i ga masu buƙata ta musamman, Yaƙi da Jahilci ta hanyar koyon sana’o’in hannu, da kuma shirin wayar da kai da ba da shawarwari ga waɗanda ke gidajen gyara hali da waɗanda suka fito daga can. 

Ya kuma sanar da shirin ciyar wa na watan azumin Ramadan na wannan shekara, inda ya yi kira ga ‘yan Siyasa, ‘Yan kasuwa, Manoma da sauran masu ruwa da tsaki a ƙaramar Hukumar Zaria da su tallafa domin ciyar da marasa galihu.

A nasa jawabin, Hon. Shuaibu Abdullahi Mai Kanta ya nuna jin dadin sa bisa karramawar da aka yi masa. 

Ya ce Gwamnati kadai ba za ta iya biyan buƙatun kowa ba, don haka ya jaddada muhimmancin ƙungiyoyin agaji da masu hannu da shuni su rika tallafa wa al’umma.

Ya ce irin waɗannan Gidauniyoyi sun fi sanin inda marasa Lafiya, Gajiyayyu da marasa ƙarfi suke, don haka suna kai ɗauki kai tsaye.

Ya ambaci misalin wata mai arziki da ta yi alƙawarin bayar da kusan Naira Miliyan 10 domin gina ɗakin taro ga Gidauniyar bayan ta ga ayyukanta. 

Ya shawarci mambobin Gidauniyar da su ci gaba da aikinsu don Allah, yana mai cewa ladan hakan yana nan a gaba.

A madadin Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad, Sakataren Yada Labarai Ishaq Galadima ya yaba da ƙoƙarin Gidauniyar da Sakataren wajen samar da cigaba a cikin al’umma. 

Ya ce ƙaramar hukumar na aiki tukuru domin inganta jin dadin al’umma, bisa jagorancin Gwamnatin Jihar Kaduna da kuma Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen.

A karshen taron, Gidauniyar ta kuma karrama wasu fitattun mutane da lambobin yabo saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban al’umma, ciki har da Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria, Barrister Aisha Muhammad, da Hon. Ismail Yesko da sauran su.

Post a Comment

0 Comments