Daga Hassan Ibrahim
Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Idris Kusfa Zaria (Rigi-Rigi) rasuwa, bayan ya sha fama da jinya.
Marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke cikin garin Kaduna a safiyar ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da sallar jana’izarsa a yau Litinin da misalin Ęarfe 4:30 na yamma, a Kusfa da ke Zariya.
Sheikh Usman Idris ya rasu yana da shekaru 56 a duniya, ya bar mata huÉu da ’ya’ya 37, kamar yadda Sagir Éan Sardauna ya shaida wa Daily Naija Updates.
Muna roĘon Allah MaÉaukakin Sarki ya jikansa, ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma sanya Aljannah Firdausi ta zama makomarsa, Aameen.

0 Comments