Header Ads Widget

 


Jaridar Taskira Ta Karrama Kansilan Dambo, Hon. Kabir Mohammed Kakeyi Da Lambar Yabo


Daga Hassan Ibrahim 


Jaridar Taskira ta karrama kansila mai wakiltar gundumar Dambo a ƙaramar hukumar Zaria, Hon. Kabir Mohammed Kakeyi, da lambar yabo bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma da kyautata zamantakewa.

An gudanar da bikin karramawar ne a ranar Asabar, 15 ga watan Maris, 2026, a cibiyar matasa da ke gundumar Tudun Wada a ƙaramar hukumar Zaria.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan karɓar lambar yabon, Hon. Kabir Mohammed Kakeyi ya bayyana cewa ba zai iya bayyana irin godiyar da yake yi wa jaridar Taskira ba.

Ya ce abin da ya fi burge shi shi ne yadda jaridar ke gudanar da ayyukanta ba tare da la’akari da dukiyar mutum ko abin da zai bayar ba, sai dai suna karrama mutane ne bisa jajircewa da kokarin da suke yi wajen hidimtawa al’umma.

Hon. Kabir Mohammed Kakeyi ya ƙara da cewa nasarorin da yake samu a fannin taimakon jama’a sun samu ne sakamakon hadin kai da kuma goyon bayan manyan shugabanni da Allah ya hada su da su.

Ya ambaci wasu daga cikin shugabannin da suke ba shi goyon baya, ciki har da Shugaban Majalisar Wakilai ta Kasa, Dakta Abbas Tajuddeen, da kuma Shugaban ƙaramar hukumar Zaria, Injiniya Jameel Ahmad Jaga, yana mai cewa duk irin taimakon da yake samu daga Allah ne amma ta karkashin jagorancin wadannan shugabanni.
A ƙarshe, Hon. Kabir Mohammed Kakeyi ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da sanya ƙasar Najeriya da shugabanninta cikin addu’a, domin Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu na jagorantar al’umma yadda ya kamata.


Post a Comment

0 Comments