Daga Hassan Ibrahim
Dan takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari a jam’iyyar ADC, Hon. Hassan Salihu Sandas Dan Rimin GRA, ya kaddamar da kwamitin tattaro magoya baya domin tabbatar da nasara a zaɓen fidda gwani da jam’iyyar za ta gudanar nan gaba.
Da yake jawabin maraba a wajen taron, Hon. Hassan Salihu ya bayyana jin daɗinsa bisa irin soyayya, zumunci da amincewa da al’umma suka nuna masa ta hanyar halartar taron cikin dimbin yawa.
Ya ce wannan rana za ta kasance abin tunawa a tarihinsa na siyasa, tare da alƙawarin ci gaba da yi wa al’umma aiki da gaskiya da riƙon amana.
A nasa jawabin, Alhaji Bashir, jakadan jam’iyyar ADC a jihar Kaduna, ya bayyana ɗan takarar a matsayin mutum mai jajircewa da kishin matasa da cigaban al’umma.
Ya yi masa fatan alheri tare da kira ga magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da haɗin kai domin samun nasara.
Hakimin Ibira da ke Sabon Gari, Alhaji Sulaiman Ibrahim, ya jaddada bukatar samun sauyi a Nijeriya ta hanyar bai wa matasa dama su jagoranci al’umma a matakai daban-daban na siyasa.
Ya ce suna shirye su mara wa ɗan takarar baya tare da ci gaba da addu’o’in samun nasara.
Shi ma wakilin masu buƙata ta musamman, Ibrahim Aliyu, ya bayyana cewa ɓangaren masu buƙata ta musamman suna tare da ɗan takarar dari bisa dari saboda yadda yake mutunta su da kuma fahimtar darajarsu a cikin al’umma.
A nasa jawabin, Alhaji Rufa’i ya yi kira ga mambobin kwamitin da aka ƙaddamar da su da su jajirce wajen ganin an samu nasara musamman a zaɓen fidda gwani da sauran zaɓukan da ke tafe.
Haka kuma, Hajiya Mariya, Hajiya Rashidat da Hajiya Najaatu sun yaba da kyawawan dabi’u da halayen ɗan takarar tare da bayyana farin cikinsu kan wannan mataki.
Sun kuma yi kira ga mata da sauran magoya baya da su haɗa kai wajen tabbatar da nasarar ɗan takarar a zaɓukan da ke gaba.

0 Comments