Header Ads Widget

 


Shugabannin Ƙananan Hukumomin Kaduna Sun yi martani kan rahoton Sahara Reporters, tare da Jaddada Goyon Bayansu Ga Uba Sani



Daga Hassan Ibrahim 


Shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna sun yi watsi da rahoton da Sahara Reporters ta wallafa, wanda ya zargi gwamnatin jihar da riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi da kuma tauye ‘yancin gudanarwar kansiloli.

Da yake jawabi a madadin shugabannin ƙananan hukumomin, shugaban ƙungiyar ALGON na jihar Kaduna, Abubakar Jamilu Albani, ya bayyana rahoton a matsayin “ƙarya, yaudara da maras tushe,” yana mai cewa bai dace da haƙiƙanin yadda ake tafiyar da ƙananan hukumomi a jihar ba.

Rahoton Sahara Reporters ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kaduna ce ke sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi maimakon a tura su kai tsaye zuwa asusun kansilolin. Haka kuma rahoton ya ce duk da cewa kowace ƙaramar hukuma na karɓar tsakanin Naira miliyan 500 zuwa 600 daga asusun tarayya, ana ba su tsakanin Naira miliyan 25 zuwa 30 ne kawai domin gudanar da ayyuka.

Sai dai Hon. Albani ya musanta zarge-zargen gaba ɗaya, yana mai cewa ƙananan hukumomin jihar Kaduna na biyan albashin ma’aikatansu tare da gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan daga gwamnatin jihar ba.

“Mun yi watsi gaba ɗaya da wannan rahoto da dukkan zarge-zargen da ke cikinsa. Ƙananan hukumomi ba sa karɓar Naira miliyan 25 kamar yadda aka bayyana, kuma gwamnatin jihar ba ta riƙe mana kuɗaɗenmu,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 23 na ci gaba da mara wa gwamnatin Uba Sani baya, tare da yabawa gwamnan bisa abin da ya kira shugabanci na adalci, ayyukan raya ƙasa da manufofin da suka shafi jama’a.

Albani ya kuma buƙaci al’ummar jihar Kaduna da su yi watsi da rahoton, yana mai cewa manufarsa ita ce haddasa ruɗani da karkatar da gaskiyar alaƙar da ke tsakanin gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi.







Post a Comment

0 Comments