Header Ads Widget

 


Jaridar Taskira Ta Karrama Hajiya Halima Abubakar Imam Bisa Gudunmawar Da Take Bayarwa Ga Al’umma


Daga Hassan Ibrahim 

Jaridar Taskira ta karrama magatakarda na Kotun Gargajiya (Customary Court) da ke Kings Road, Sabon Gari Zariya, Hajiya Halima Abubakar Imam, bisa irin gudunmawar da take bayarwa wajen hidimtawa al’umma ta fuskar aikinta.

An gudanar da bikin karramawar ne a ranar Asabar, 6 ga Yunin 2026, a Cibiyar Matasa da ke Tudun Wada, Zariya, inda ‘yan uwa, abokan arziki da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta domin nuna goyon baya da girmamawa ga wadda aka karrama.

Da take jawabi jim kadan bayan karbar lambar yabo, Hajiya Halima Abubakar Imam ta bayyana farin cikinta da godiyarta ga Jaridar Taskira bisa ganin ta cancanci wannan karramawa.

Ta ce aikin da suke yi hidima ce ga al’umma, don haka za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya, rikon amana da jajircewa domin ci gaban jama’a.

Hajiya Halima ta kuma yi kira ga ma’aikata a dukkan bangarori da su rungumi gaskiya da amana wajen gudanar da ayyukansu, tana mai jaddada cewa wadannan dabi’u ne ginshikin cigaban kowace al’umma.

Har ila yau, ta bukaci mata da su mayar da hankali wajen tarbiyyar ‘ya’yansu tare da neman ilimi, domin samun rayuwa mai inganci da abin koyi ga al’umma.

Ta tabbatar da cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da hidimtawa jama’a, tana mai cewa hidimar al’umma na daga cikin hanyoyin samun nasara da ci gaba a rayuwa.
Bikin ya samu halartar ‘yan uwa, abokan arziki da masoya daga sassa daban-daban na cikin da wajen Zariya





Post a Comment

0 Comments