Header Ads Widget

 


Jaridar Taskira Ta Karrama Injiniya Ahmad Aminu Vertical Kan Ayyukan Alheri da Ci Gaban Al’umma


Daga Hassan Ibrahim 


Jaridar Taskira ta karrama Injiniya Ahmad Aminu Vertical, zaɓaɓɓen ɗan takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari a jam’iyyar ADC, bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa rayuwar al’umma ta fannoni daban-daban.

An gudanar da bikin karramawar ne a ranar Alhamis, 11 ga Yuni, 2026, a Cibiyar Matasa da ke Tudun Wada a Zariya, inda taron ya samu halartar ‘yan uwa, abokan arziki da kuma magoya bayan ɗan takarar daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar Sabon Gari.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan karɓar lambar yabon, Injiniya Ahmad Aminu Vertical ya bayyana matuƙar farin cikinsa tare da miƙa godiyarsa ga Jaridar Taskira bisa wannan karramawa da ta yi masa, yana mai yi wa ma’aikatan jaridar fatan alheri.

Ya ce wannan karramawa ba dabara ba ce ko kuma wayau, illa wata ni’ima ce daga Allah da kuma lokacin da Ya ƙaddara, wanda al’umma suka gani kuma suka shaida.
A cewarsa, bai yi tsammanin samun wannan lambar yabo ba, sai dai Allah Madaukakin Sarki ne Ya ƙaddara hakan bisa ayyukan alherin da yake yi wa al’ummar ƙaramar hukumar Sabon Gari.

Ya ƙara da cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da suka shafi walwalar jama’a, yana mai addu’ar Allah Ya ba shi ikon ci gaba da hidimtawa al’umma.

Injiniya Ahmad Aminu Vertical ya bayyana cewa sun ba da muhimmanci sosai ga fannin ilimi da bunƙasa matasa, yana mai cewa suna ci gaba da bayar da gudunmawa domin tabbatar da cewa matasa sun samu kyakkyawar makoma.

Ya ce sun bayar da gudunmawa sosai wajen tallafa wa matasa da nufin tabbatar da haɗin kai da ci gaban al’umma.

A fannin sana’o’i kuwa, ya ce sun horas da matasa da dama kan sana’o’in zamani, musamman waɗanda suka shafi harkokin lantarki da makamashi, tare da jaddada cewa za su ci gaba da faɗaɗa irin waɗannan shirye-shirye domin samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ya kuma bayyana cewa idan Allah Ya ba su nasara a zaɓen majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari, suna da tsare-tsare masu inganci da za su kawo ci gaba wanda al’umma za su amfana da shi.

A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya ba su jagora tare da tabbatar musu da nasarar cimma manufofin da suka sanya a gaba.

Haka kuma ya miƙa godiya ta musamman ga al’ummar ƙaramar hukumar Sabon Gari, maza da mata da matasa, bisa goyon baya da addu’o’in da suke ci gaba da ba su.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu a lokacin babban zaɓe domin kaɗa ƙuri’unsu ga jam’iyyar ADC daga sama har ƙasa.



Post a Comment

0 Comments