Header Ads Widget

 


JAGORORIN APC NA SABON GARI SUN AMINCE DA ‘YAN TAKARAR DA AKA TSAYAR GABANIN FARA ZABEN FIDDA GWANI


Daga Hassan Ibrahim 

Jagororin jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari sun amince baki ɗaya da ‘yan takarar da aka tsayar gabanin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar.

An cimma wannan matsaya ne a wani muhimmin taro da Shugaban Karamar Hukumar, Sheikh Jamilu Abubakar Albani, ya jagoranta, wanda ya hada manyan shugabannin jam’iyya, dattawa, masu rike da mukaman siyasa, wakilan matasa da mata, da kuma wakilan gundumomi daga sassa daban-daban na karamar hukumar.

A cikin wata sanarwar manema labarai da Aminu Abu Zayd, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai na Ofishin Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari ya fitar, ya ce jagororin sun sake jaddada kudurinsu na tabbatar da hadin kai, kwanciyar hankali, da cigaban jam’iyyar a dukkan matakai, inda ya bayyana cewa amincewar da aka yi wata dabara ce ta karfafa dankon zumunci da hadin kan APC a yankin.

‘Yan takarar da aka amince da su sun hada da Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar Shugaban Kasa, Uba Sani a matsayin dan takarar Gwamna, Mukhtar Ramalan Yero a matsayin dan takarar Sanata, Sadiq Ango Abdullahi a matsayin dan takarar Majalisar Wakilai, Nasiru Idris a matsayin dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar Sabon Gari, da kuma Sani Dahiru Basawa a matsayin dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar Basawa.

Jagororin sun bayyana cewa wannan amincewa na nuna cikakken yarda da kwarewa, nagarta, da jajircewar ‘yan takarar wajen bayar da ingantacciyar wakilci da kawo cigaba mai ma’ana ga al’umma. 

Sun kuma bayyana cewa wannan mataki wata muhimmiyar hanya ce ta tabbatar da dorewar shugabanci da kuma kara karfin jam’iyya a zaben fidda gwani da kuma babban zabe mai zuwa.

A karshe, taron ya kammala da tsayayyen kuduri cewa wannan matsaya ita ce hukunci na karshe da jagororin APC na Sabon Gari suka dauka domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, cigaba, da nasarar jam’iyyar baki daya, tare da alkawarin ci gaba da wayar da kai da tara goyon baya ga dukkan ‘yan takarar da aka amince da su a dukkan matakan zabe.

Post a Comment

0 Comments