Header Ads Widget

 


Shugabar Mata ta ADC a Shiyya ta Ɗaya Kaduna Ta Yi Magana Kan Yawaitar Masu Shiga Jam’iyya, Tare da Kira ga Sauyi


Daga Hassan Ibrahim 


Hajiya Murjanatu Abdul Hassan, shugabar mata ta jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a shiyya ta ɗaya ta jihar Kaduna, ta ce yawaitar shigowar jama’a cikin jam’iyyar na nuna yadda mutane suka gaji da halin ƙuncin rayuwa tare da neman mafita.

Ta bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da ita a Zaria, inda ta ce a kullum jama’a na tururuwa suna shiga jam’iyyar daga sassa daban-daban na al’umma, ciki har da matasa maza da mata, suna halartar taruka tun daga matakin gunduma har zuwa shiyya ta ɗaya.

A cewarta, mutane da dama na jan hankalinsu ne da kyawawan tsare-tsaren jam’iyyar da kuma yadda take bai wa al’umma dama su shiga harkokinta.

Hajiya Murjanatu ta lura cewa har yanzu mata ba su farka sosai wajen fahimtar ƙarfinsu a harkokin siyasa ba. 

Ta ƙara da cewa wasu daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar sun nuna jajircewa wajen cigaban al’umma, inda ta bayar da misalin wani mai taimakon jama’a da ya horas da kusan matasa 3,000 sana’o’in hannu domin su dogara da kansu.

Ta ce babban burin jam’iyyar ADC shi ne fitar da talaka daga halin ƙunci tare da samar masa da hanyoyin inganta rayuwa.

Saƙonta ga jama’a shi ne su kasance masu wayewa, su fahimci yanayin da ake ciki, tare da neman sauyi cikin hikima da addu’a.

Da take tsokaci kan yanayin ƙasa gaba ɗaya, ta buƙaci jama’a su kasance masu lura da al’amuran da ke faruwa tare da fatan samun shugabanci mai adalci da gaskiya.

Ta kuma yi addu'ar samun mafita ga shuwagabannin su da ke tsare, tare da addu'ar ya karesu baki ɗaya.

Baya ga harkokin siyasa, Hajiya Murjanatu ta shahara a Zariya da kewaye wajen tallafawa marayu maza da mata tsawon lokaci ta hanyoyi daban-daban.

Post a Comment

0 Comments