Daga Hassan Ibrahim
Zaria ta shaida wani gagarumin shiri na tallafawa matasa inda akalla matasa maza da mata 3,000 aka horas da su sana’o’i daban-daban tare da ba su jari domin su dogara da kansu a dukkanin gundumomi 13 na ƙaramar hukumar.
An gudanar da bikin yaye waɗanda suka amfana a dakin taro na Sultan Muhammad Bello da ke kwalejin Barewa , inda manyan baki, shugabannin al’umma, ‘yan siyasa da mata masu ruwa da tsaki suka halarta tare da yaba wa wannan shiri.
Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Tukur Salisu Kakeyi ya bayyana matuƙar jin daɗinsa kan yadda wani bawan Allah ya ware wani kaso daga dukiyarsa domin horas da matasa sana’o’i tare da ba su jari.
Ya yi kira ga masu hali a cikin al’umma da su yi koyi da irin wannan kyakkyawan hali, sannan ya buƙaci waɗanda aka horas da su riƙe sana’o’in da kyau domin suma su amfanar da wasu.
Shi ma Hon. Suleiman Ibrahim Dabo, wakilin Birnin Zazzau, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa sana’o’in hannu su ne ginshiƙin cigaban al’umma, musamman ganin yadda matasa da dama ke karatu amma ba su da ƙwarewar sana’o’i.
Basaraken ya jaddada cewa taimakon al’umma bai kamata ya tsaya ga ‘yan siyasa kaɗai ba, ya ce ya dace masu hali su riƙa taimakawa domin rage matsalolin da ke haifar da sata da shaye-shaye sakamakon rashin aikin yi da damuwa.
Injiniya Abubakar wanda aka fi sani da “NEPA” ya ce abin da ya fi ba shi sha’awa shi ne yadda matasa da dama da ke zaman banza a gida yanzu suka samu abin yi ta hanyar koyon sana’o’i.
Murjanatu Abdul Hassan, shugabar mata ta jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) shiyya ta ɗaya a jihar Kaduna, ta bayyana farin cikinta bisa sauyin da ta gani a rayuwar matasa, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su tsaya da ƙafafunsu ta hanyar amfani da sana’o’in da suka koya.
Mai ɗaukar nauyin shirin, Aliyu Lawal Ibrahim wanda aka fi sani da Ali Cairo, ya bayyana cewa wannan tunani ya samo asali ne daga halin ƙuncin rayuwa da al’umma ke ciki, musamman a Zariya.
Ya ce ba kowa ne zai samu aikin gwamnati ba, don haka koyar da sana’o’i ita ce mafita.
Ya bayyana cewa an horas da matasa sana’o’i kamar ɗinki, haɗa takalma, yin jaka, yin turare, yin man shafawa da madarar jiki da sauransu.
Ya kuma ce an ware naira dubu 500 a kowace gunduma domin horaswa, inda malamai ke zagayawa daga gunduma zuwa gunduma. Duk waɗanda aka tabbatar sun ƙware, za a haɗa su gida-gida a ba su jari domin fara sana’ar su.
Ali Cairo ya nuna matuƙar tausayawa da jin daɗi kan yadda jama’a ke yi masa addu’a musamman ga mahaifiyarsa da mahaifinsa Malam, abin da ya ce ba zai taɓa mantawa da shi ba.
Ya kuma ƙara da cewa idan Allah ya ba shi dama ya je Majalisar Tarayya, yana da tsare-tsaren faɗaɗa irin wannan shiri domin inganta rayuwar al’umma.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin, ciki har da Aliya daga Kofar Kuyambana da A’isha Abdullahi, sun bayyana godiyarsu da farin cikinsu, suna mai cewa wannan shiri ya sauya musu rayuwa.
Wannan biki ya zama bikin yaye na waɗanda suka amfana ƙarƙashin gidauniyar Ali Cairo tare da haɗin gwiwar cibiyar koyar da sana’o’i ta Zaria, wanda ya zama wani babban mataki na ƙarfafa matasa su dogara da kansu da kuma cigaban al’umma.

0 Comments