Daga Hassan Ibrahim
Sanata Khalid Ibrahim Mustapha, wanda aka fi sani da Khalid Soba, ya zama ɗan takarar Sanatan Kaduna ta Arewa (Zone 1) na jam’iyyar ADC bayan kammala zaɓen fidda gwani cikin lumana da aka gudanar a faɗin yankin a ranar Asabar.
Da yake sanar da sakamakon zaɓen, Jami’in Tattara Sakamako na Zone 1 kuma mamba a kwamitin gudanar da zaɓen jam’iyyar ADC, Ibrahim Sidi Bamali, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya, adalci da kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
Ya ce rahotannin da aka samu daga ƙananan hukumomi takwas da suka shiga zaɓen sun nuna cewa babu wani rikici, barazana ko cin zarafi da ya faru a yayin gudanar da zaɓen.
“Mun gudanar da zaɓe cikin lumana ba tare da wata hayaniya ba. Babu rikici, babu tsoratarwa ko wata matsala. Bayan karɓar rahotanni daga dukkan jami’anmu tare da tabbatar da cika ƙa’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, mun ayyana Sanata Khalid Ibrahim Mustafa a matsayin wanda ya samu nasara kuma ya zama ɗan takarar jam’iyyar,” in ji Bamali.
Jami’in ya bayyana cewa Khalid Soba, wanda shi kaɗai ne ya tsaya takara a zaɓen, ya samu gagarumin goyon baya daga dukkan ƙananan hukumomin yankin.
Sakamakon ya nuna cewa ƙaramar hukumar Ikara ta ba shi ƙuri’u 11,226, Kudan 7,090, Makarfi 6,368, Sabon Gari 6,924, Lere 6,217, Soba 10,237, Zariya 27,325, yayin da Kubau ta ba shi ƙuri’u 7,683.
Jimillar ƙuri’un da ya samu ta kai 83,070, abin da ya tabbatar da nasararsa a zaɓen fidda gwanin.
Bamali ya ƙara da cewa duk da cewa kwamitin zaɓen na Zone 1 ya kammala aikinsa tare da bayyana sahihin sakamakon zaɓen, sanarwa ta ƙarshe da tabbatar da ɗan takarar za a yi ne a matakin jiha ta hannun Jami’in Tattara Sakamakon Jiha na jam’iyyar ADC.
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, suna mai bayyana hakan a matsayin alamar haɗin kai da bin tafarkin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar gabanin babban zaɓen da ke tafe.
Da wannan sakamako, Sanata Khalid Ibrahim Mustafa ya zama zakaran takarar ADC na Sanatan Kaduna ta Arewa, inda zai jagoranci jam’iyyar a fafatawar zaɓe mai zuwa.

0 Comments