Daga Hassan Ibrahim
Jaridar Taskira ta karrama Barrister Aisha Iyal Waziri a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, 2026, bisa jajircewarta wajen gudanar da aikinta tare da gudummawar da take bayarwa ga al’umma ta fuskar hidimar shari’a da gudanarwa.
Barrister Aisha Iyal Waziri, wadda ke aiki a matsayin Magatakardar Upper Sharia Court III, ta bayyana farin cikinta da godiyarta ga Allah Madaukakin Sarki bisa damar da ta samu na karÉar wannan lambar yabo, tare da miĘa godiya ga Jaridar Taskira saboda ganin ta cancanci wannan girmamawa.
Ta bayyana cewa samun irin wannan karramawa bisa cancanta yana da matuĘar muhimmanci ga duk wani ma’aikaci, domin yana Ęara masa Ęwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da aikinsa cikin gaskiya, riĘon amana da kuma tsoron Allah.
Barrister Aisha ta jaddada cewa ita da abokan aikinta suna ĘoĘarin ganin an tabbatar da tsafta da inganci a harkokin aiki, tana mai cewa da taimakon Allah suna yin iya ĘoĘarinsu wajen sauke nauyin da aka Éora musu yadda ya kamata.
Ta kuma bayyana cewa tana yawan bai wa ma’aikatan da suka yi aiki tare da ita shawara da su kasance masu haĘuri, lura da Ęananan bayanai da kuma mai da hankali ga abubuwan da suka shafi aikin kotu, domin waÉannan su ne ginshiĘan nasara a aikin shari’a da gudanarwa.
A cewarta, abin da ta fi so shi ne ganin ma’aikaci ya tsaya tsayin daka wajen gudanar da aikinsa cikin Ęwazo da gaskiya tare da tabbatar da adalci ga al’umma.
Ta Ęara da cewa tsoron Allah shi ne mataki na farko na nasara ga kowane ma’aikaci, yayin da jajircewa da riĘon amana suke zama tubalan ci gaba da Éaukaka a rayuwa da kuma a wurin aiki.
“Tsoron Allah da jajircewa a aiki su ne manyan saĘonnin da nake son isarwa ga kowane ma’aikaci,” in ji Barrister Aisha Iyal Waziri.

0 Comments