Header Ads Widget

 


Zakariyau Barde Ya Yabawa Sakataren Karamar Hukumar Zariya Kan Shirin Tallafa wa Al'umma, Ya Bukaci a Kara Bai wa Jama'a Kulawa


Daga Hassan Ibrahim 


Mataimaki na Musamman kan Harkokin Filaye ga Gwamnan Jihar Kaduna, Zakariyau Barde, ya yabawa Sakataren Karamar Hukumar Zariya, Honarabul Shu'aibu Abdullahi Mai Kanta, bisa kokarinsa na tallafa wa al'umma ta hanyar shirye-shiryen inganta rayuwar jama'a daban-daban.

Da yake zantawa da manema labarai yayin rabon kayan tallafi da Sakataren Karamar Hukumar ya shirya, Zakariyau Barde ya bayyana jin dadinsa kan wannan mataki, tare da kira ga 'yan siyasa da su ci gaba da taimaka wa marasa galihu, yana mai cewa addinin Musulunci yana karfafa irin wadannan ayyuka kuma suna da lada mai yawa.

Ya ce farin ciki da annashuwar da aka gani a fuskar wadanda suka amfana da tallafin na nuna irin tasirin da shirin ya yi ga rayuwar jama'a. Ya kara da cewa jam'iyyar APC jam'iyya ce da ta shahara wajen cika alkawura da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta ga al'umma.

A cewarsa, shugabanci da jajircewar Gwamna Uba Sani wajen kyautata rayuwar al'umma sun zaburar da masu rike da mukaman gwamnati da dama su ci gaba da taimakawa tare da cike gibin kokarin gwamnati.

Ya bayyana rabon filaye ga mazauna unguwar Alhuda Huda, wadanda aka rusa gidajensu a zamanin gwamnatin da ta gabata, a matsayin daya daga cikin ayyukan jin kai da Gwamna Uba Sani ya aiwatar domin rage radadin da jama'ar suka fuskanta.

Hakazalika, Zakariyau Barde ya yi kira ga al'ummar Karamar Hukumar Zariya da su ci gaba da bai wa Gwamna Uba Sani goyon baya tare da yi masa addu'ar samun nasara wajen aiwatar da manufofinsa na ci gaban jama'a, yana mai jaddada cewa babu wata karamar hukuma a Jihar Kaduna da ke samun irin kulawa da mayar da hankali kan ci gaba daga wajen gwamnan kamar Karamar Hukumar Zariya.

Post a Comment

0 Comments